Saboda tsoron Ebola, kabilu da yawa sun daina cin namun daji na mafarauta, watau bushmeat
- Labarai daga kasar Congo mai tsoratarwa kan Ebola
- Ana cin naman daji kamar birrai da jemage a tsakanin kabilun Afirka
- Yanzu mutane na tsoro
A birnin Mbandaka, naman dabbobin daji arha yake, ana kuma amfani dashi a matsayin abinci. Birai, jemage, shirwa, kada da sauran namomin daji.
Amma masu tallar naman sunce, basa samun kasuwa sakamakon barkewar Ebola a arewa maso yammacin jamhuriyar Congo.
Masana kimiyya sunce naman dabban daji mai dauke da ciwon Ebola yana iya yada cutar. A yayin da wasu 'yan gargajiya ke danganta cutar da tsafi.
"Kasuwar mu ta mutu" inji Sebastien Nseka Lokila, wanda ke shugabantar babbar kasuwar birnin mai mutane miliyan 1.2. Yace basa samun naman daga Bikoro, wani kauye ne a tsakiyar inda cutar ta barke.
DUBA WANNAN: Iyaye sun kai karar gardi da yaki barin gidansu bayan sun raine shi shekaru 31
Tsirarun masu siyan naman suke siya a ranar talata. Masu tallan naman sun yayyanka naman ba tare da safar hannu ba suna tattaba naman. Wannan yana nuna cewa an saukar da farashin naman.
"Ina son naman dabbobin daji, baya kawo cutar komai." inji Nelly Mboyo, wata magidanciya a kasuwar. Amma wasu matan wuce naman sukeyi ba tare da tsayawa don siye ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng