Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu

Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu

- Kwankwasiyya ce ta kawo tsarin ciyarwa a makarantu a 1999 da 2011

- Shuwagabannin APC sun kwaikwayi shirin a jihohin Tarayya

- Yanzu abin ya bunkasa jihohi har 24, da dalibai miliyan takwas

Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu
Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu

Sabon salo, iya cika alkawari, a wannan karon dai za'a iya cewa gwamnati ta cika alkawari da ta debo a 2014

Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu
Sabon rahoto: Yawan dalibai da gwamnatin Tarayya ta APC ke ciyarwa da kuma yawan jihohin sun karu

Gwamnatin tarayya tana ciyar da daliban firamare 8,260,984 a makarantun firamare na gwamnati 45,394 a jihohi 24 a karkashin shirin National Home Grown School Feeding, ofishin shuwagabancin Kasar ya bayyana a ranar laraba.

Babban mai bada shawara na musamman ga mataimakin shugaban kasa akan yada labarai, Laolu Akande, yace yawan yaran ya wuce yanda aka yi nufi, wato miliyan 5.5.

Jihohin 24 sun hada da :Anambra, Enugu, Oyo, Ogun, Ebonyi, Zamfara, Delta, Abia, Benue, Plateau da jihohin Bauchi. Sauran sun hada da Taraba, Kaduna, Akwa IBM, cross river, Imo, jigawa, Niger, Kano, katsina, Gombe, Ondo da Borno.

Kamar yanda yace, an samar da aikin yi sama da 80,000 sakamakon aikin ciyar da yaran.

Ya kara da cewa jihohin kasar guda 36 da kuma birnin tarayya zata amfana da shirin ciyar da daliban.

"Shirin ciyar da daliban firamare na karkashin mulkin Buhari ba wai samar da aikin yi ga mutane kadai tayi ba. A'a, ya taimaka gurin habako da kananan tattalin arziki, ta hanyar hada manoma da ciyarwar."

"Haka kuma, ciyar da daliban ya cigaba da samar da karin dalibai. Wani abu mai muhimmanci na ciyarwar shine samar wa da miliyoyin mutane abinci. Inda ya magance matsalar rashin ingantaccen abinci ga yara, wanda zai kara kawo kwazo na yaran gurin karatu."

DUBA WANNAN: Iyaye sun kai karar gardi da yaki barin gidansu bayan sun raine shi shekaru 31

Wannan dai a iya cewa duk da Kwankwasiyya ce ta kawo shi, an sami ci gaba sosai wajen cika alkawari da ta dauko a lokutan zaqin baki na Kamfe kan ciyar da yara a makaranta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng