Wani gardi da ya ki barin gidan iyayensa zai bayyana gaban alkali bayan iyayen sun kai qara
- Bayan ya shekara 30 a gida, Michael ya makale iyayensa na ciyar dashi
- A tsarin Turai in mutum ya balaga, mace ko namiji yakan bar gida ya kama aiki
- Anyi-Anyidashi ya je ya kama aikin yi ko ya karbi jari amma kememe
A wani abin dariya da ba safai aje jinsa ba, an sami wani saurayi da ya zama gardi dan shekara 30 da yaki yaye daga 'maman iyayensa', anyi-anyi dashi ya tashi ya kama gidan haya amma yaki, kememe ya manne kuma baya ko aikin cikin gida na shara ko wanke-wanke.
A kokarin iyayen nasa na lallai sai yabar gida, iyayen sun rubuta masa wasika, kan wa'adin karshe ya tafi ya kama haya, da zimmar zasu bashi dala dubu domin ya iya mikewa da kafarsa, sai dai ya shallake wa'adin yaki tafiya.
A tsari dai in ka balaga, mace ko namiji, akan sa rai zaka fita ka kama gidan haya doomin neman na kanka ko kanki, ko tarewa da masoyi, a kasashen waje.
DUBA WANNAN: Sabbin nade-naden da shugaba Buhari yayi a yau
Yanzu dai batun rigimar wadannan iyaye da dansu ta kai gaban kotun koli a kasar Amurka don ganin an raba kato da manne wa a gida, baya shuka fari balle baki.
Ko shekaru nawa ne a yankin ku na yadda budurwa koo saurayi zasu bar gida suyi zaman kansu? tafka muhawara a kasa.
Labari daga shafin BBC Hausa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng