Dalilan da su ke sa yaki da rashin gaskiya yake wahala a Najeriya
Shugaban Kasa Muhammadu yayi alkawarin yaki da masu satar dukiyar kasa idan ya hau mulki lokacin da yake neman kujerar. Sai dai abin bai zo masa da sauki ba kamar yadda yake tunani. Kungiyar SERAP ta bayyana inda ake samun matsaloli.
Daga cikin yadda marasa gaskiya ke tserewa shari’a akwai:
1. Yi wa Kotu gardama wajen shari’a
2. Kalubalantar hurumin Kotu kafin a fara bincike
3. Gibi a dokokin kasa
4. Rashin amincewa da maganar Kotu
KU KARANTA: Halayen Shugaba nagari guda (4) inji Obasanjo
5. Kariya daga dokar kasa
6. Karyar rashin lafiya da lambo
7. Rashin iya shigar da kara
A halin yanzu musamman tsofaffin Gwamnonin Kasar kan yi amfani da daya ko wasu daga cikin wadannan dabaru wajen hana a bincike su yadda ya dace. Wasu kan daukaka kara su na kalubalantar zaman shari’a tun kafin ayi nisa.
Ana kuka kuma da gibin da yake tsarin dokokin kasar tare da kuma amfani da kariya daga bincike da dokar Kasa ta ba wasu masu mulki. Bayan nan kuma har wasu da ake zargi kan yi lanbo ban da rashin kwarewar Hukumomin binciken kasar.
A jiya Shugaba Muhammadu Buhari yace a lokacin da yake mulkin Soji sai da ya kama duk Shugabannin kasar nan ya daure saboda zargin sata illa wanda ya iya karbar kan sa. Sai dai yace a tsarin Damukaradiyya sam hakan ba zai yiwu ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng