Obasanjo ya zayyana halayen shuagaba nagari guda 4
Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya zayyana wasu halaye guda hudu da ya ce dole duk wani shuagaba da yake ikirarin shi nagari ne dole ya kasance yana da su.
Obasanjo ya bayyana hakan ne yayin gabatar da lakca a jami’ar jihar Legas (LASU) a wurin bikin yaye daliban makarantar.
A cewar Obasanjo, dole shugaba ya samar da jagoranci na gari, ya samar da gwamnati ta gari, ya kawowa jama’a cigaba da kuma ciyar da kasa gaba.
Obasanjo ya kara da cewa dole a inganta ilimin gaba da sakandire domin samun shugabanni nagari da zasu ceci Najeria.
A nasa jawabin, gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode, y ace ya kamata jami’o’I su fara cusawa dalibai dabarun shugabanci domin samun cigaba mai dorewa a kasa.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisar zartarwa na yau (Hotuna)
A nasa bangaren, shugaban hukumar kula da jami’o’I na kasa, Farfesa A.A Rasheed ya bayyana cewar lokaci ya yi da jami’o’in kasar nan zasu fara bayar da muhimmiyar gudunmawa domin cigaban tattalin arzikin Najeriya ta hanyar bawa ilimin fasaha fifiko.
“Me yasa zamu ke yaye dalibai a bangaren fasahar kere-kere da gine-gine amma gwamnati na cigaba da kasha kudi domin dauko injiniyoyi da zasu gina mana hanyoyi? Me yasa jami’o’I zasu cigaba da kasha makudan kudi a kan samar da wutar lantarki maimakon bullo da hanyoyin da zasu samarwa kan su lantarki?,” a ceware Farfesa Rasheed.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng