Ku tsame ni cikin batun sace Sandar Majalisa domin babu hannu na ciki - Ndume
- Bayan bayyawa gaban Kwamitin bincike da Majalisa ta kafa kan sacce Sandar Iko da wasu Matasa su kayi, Sanata Ndume ya musanta cewa yana da hannu ciki
- Takwaransa da ake tuhumarsu tare ya ki cewa komai ga kwamitin
Sanata Ali Ndume daga jihar Borno ya musanta zargin taimakawa wasu ‘yan daba yin kutse gami da sace Sandar ikon Majalisar.
An dai rawaito cewa Sanatan ya umarci Jami'an da suke bakin aiki a ranar da lamarin ya faru a watan da ya gabata da kada su kuskura su taba sandar, wanda hakan ya bawa Matasan damar tserewa da Sandar cikin sauki
Da yake magana gaban kwamitin da Majalisar kasa ta kafa domin bincikar yadda balahirar ta faru, Ndume ya musanta bayan da wancan umarnin.
Shima takwaransa da ake tuhumar su tare Sanata Ovie Omo-Agege yayi kememe wajen cewa komai kan maganar satar Sandar ga kwamitin.
Kafin dai fara taron an hana ‘yan Jarida shiga amma daga baya aka kira su bayan Mintuna 10, domin su shaida yadda zaman zai kasance.
KU KARANTA: Yanzu Yanzu: An sake garkuwa da fasinjoji 42 a Birnin-Gwari zuwa Kaduna Author: Abubakar Nura Bala
Bayan fara zaman ne shugaban kwamitin Sanata Bala Ibn Na’Allah ya tambayi Ndume “Shin ko da gaske ne maganar ya umarci jami’in da yake kula Sandar da kada ya dauki wani mataki bayan da hatsaniya ta fara barkewa a Majalisar.”
Sai Ndume ya kada baki ya ce, Hakika nayi mamaki da naji ana tuhumata da wannan maganar.
Tun da muke a Majalisar nan ba’a taba yi aika-aika ba kamar wannan, har a shigo a sace sandar a gudu da ita. A gani na wanann ba abu ne mai kyau da zan shiga cikinsa ba, ba zany i ba, ba zan bayar da umarni ga wani kada yayi aikinsa ba don abu ne nima da nasan bai kamata ba.”
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng