Zuwan Mohamed Salah masallacin Liverpool ya kara yawan mutane dake zuwa sallah a masallacin
- Dan kwallon Liverpool Mohamed Salah, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kwallaye na gasar zakarun nahiyar turai a shekarar 2017-2018
- Yayi nasarar jefa kwallaye 32 a wasanni 36 ga kungiyar kwallon ta Liverpool wanda yafi kowa kwallaye a raga a halin yanzu
- Zuwansa wani tsohon masallaci a Liverpool ya kara yawan mutanen dake halartar masallacin wanda ya hada da matasa da kuma tsofaffi
Dan kwallon Liverpool Mohamed Salah, ya kafa sabon tarihi a gasar cin kwallaye na gasar zakarun nahiyar turai a shekarar 2017-18, wanda ya jagoranci kungiyar kwallon zuwa gasar zakarun nahiyar turai zuwa fage na karshe a cikin shekaru 11.
Dan wasan dan asalin kasar Masar, yayi nasarar jefa kwallaye 32 a wasanni 36 ga kungiyar kwallon ta Liverpool wanda yafi kowa kwallaye a raga a halin yanzu.
Zuwansa wani tsohon masallaci a Liverpool ya kara yawan mutanen dake halartar masallacin wanda ya hada da matasa da kuma tsofaffi, wanda ya kara daga martabar addinin musulunci a fadin kasar.
KU KARANTA KUMA: Ana rikici akan kujerun ‘yan majalisa da suka rasu akan mulki
Dr. Abdul Hamid daya daga cikin malaman masallacin na Sheikh Abdullahi Quilliam yace matasa na ta kara tararowa masallacin suna gabatar da salloli a ciki harda sallar juma’a saboda Mohamed Salah, na zuwa masallacin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng