Bafarawa ya yi bude baki da limamin Makka, Sheikh Sudais (hotuna)
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa shugaban limaman masallatai biyu masu tarin alfarma na Makka da Madina, Sheikh Abdurrahman Assudais ya yi bude baki tare da manyan mutane.
Cikin manyan mutane akwai tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa wanda ya kasance abokin Sudais.
Sun sha rowan ne a masallaci mai tsarki a lokacin wannan wata mai albarka wato Ramadan.
Ga hotunan a kasa.
KU KARANTA KUMA: Zan yi mai yiwuwa game da rikicin ‘Yan Majalisa da Sufetan ‘Yan Sanda - Shugaba Buhari
Idan baza ku manta ba wannan ba shine karo na farko ba da tsohon gwamnan ke samun karramawa a kasar Saudiyya ba, domin yana daga cikin mutanenda Legit.ng ta rahoto a baya cewa an bude masu ka'aba sun shiga.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng