A lokacin da nake mulkin Soji ban jin shakkar kowa – Shugaba Buhari

A lokacin da nake mulkin Soji ban jin shakkar kowa – Shugaba Buhari

- Shugaban kasa Buhari yace sun tsinci hanyoyin kasar nan cikin halin lahaula

- Buhari yace babu wanda ya taba ware kudi kan ayyukan gina kasa kamar sa

- Shugaban yace lokacin da yake mulki a 1984 sai da ya daure barayin Najeriya

A jiya ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘Yan kungiyar BSO na Magoya bayan sa a fadar Shugaban kasar da ke Aso Villa inda ya tattauna da su kan batutuwan da su ka shafi halin kasar.

A lokacin da nake mulkin Soji ban jin shakkar kowa – Shugaba Buhari
Buhari yace IBB ya saki barayin da ya daure kuma aka zauna lafiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Gwamnatin sa na matukar kokari duk da halin da ta tsinci kan Kasar nan. Shugaban Kasa Buhari yake cewa babu Shugaban kasar da ya kashe kudi wajen gina titi da hanyoyi irin sa.

Shugaba Buhari yace Gwamnatin nan ta kashe sama da Tiriliyan 1.3 cikin bara da bana kurum domin gina hanyoyi da sauran abubuwan more rayuwa a Najeriya. Kafin nan dai an bar tituna da hanyoyin dogo sun lalace kwarai a Kasar.

KU KARANTA: Wani Kamfani ya roki Gwamnatin Buhari ta ba shi dama ya rangada aikin jirgin kasa

Bayan haka Shugaban kasar yace a lokacin da yake mulkin Soji sai da ya kama duk Shugabannin kasar ya daure saboda zargin sata illa wanda ya iya karbar kan sa. Sai dai yace a wannan tsarin Damukaradiyya sam hakan ba zai yiwu ba.

Shugaba Buhari yace da yake mulkin Soja tsakanin 1983 zuwa 1985 har Shugaban kasa sai da ya daure. Sai dai kuma bayan an kifar da Gwamnatin sa, sai da aka daure shi kan sa sannan kuma aka maidawa barayin kasar duk kudin da su ka sata.

Dama kun ji cewa Shugaban kasar ya caccaki tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo na kashe makudan kudi kan harkar wutan lantarki yace wasu titunan kuma rabon da a taba su tun lokacin da ya rike PTF a Gwamnatin Marigayi Janar Sani Abacha.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng