Shugaba Buhari ya sha ruwa da manyan hafsoshin tsaron kasa, kalli kayatattun hotunan
Shugaba Muhammadu Buhari ya shirya liyafar shan ruwa ta musamman wa manyan hafsoshin tsaron kasa da wasu ministoci bayan azumtar rana ta 6 a watan Ramadana a fadar shugaban kasa, Aso Villa da ke Abuja.
Daga cikin wadanda suka halarci wannan liyafa sune babban hafsan sojin kasa, Laftanan Janar Tukur Buratai; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar; sifeto janar na yan sanda, IGP Ibrahim Idris; NSA Ali Munguno.
Daga cikinsu akwa ministan tsaro, Mansur Dan Ali; kwantorlan hukumar kwastam, Hameed Ali; ministan harkokin cikin gida, Abdur Rahman Dambazzau; diraktan hukumar DSS, Lawal Daura.
Daga cikin ministoci akwai, ministan wutan lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Raji Fashola; ministan sadarwa, Adebayo Shittu; karamar ministar kasafin kudi, Zainab Ahmed Shamsuna; ministar harokokin mata, Aisha Jummai Alhassan.
Daga cikin ma'aikatan fadar shugaban kasa sune sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da shugaban ma'aikatan fadar, Abba Kyari.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng