Madallah: Gwamnatin Tarayya ta bayyana adadin Kudade na rarar Ma'aikatan Bogi
A ranar talatar da ta gabata ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana adadin kudade da gwamnatin sa ta samu na rara ma'aikatan bogi cikin ma'aikatun gwamnati wanda a halin yanzu ta adana inda za a ci moriyarsu a wani bangaren.
Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, shugaba Buhari ya bayyana cewa kimanin sama da N120bn gwamnatin sa ta samu na rara bayan ta rairaye ma'aikatan bogi a kasar nan daga ma'aikatun gwamnati.
Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa, gwamnatin sa ta samu rara ta N108bn a halin yanzu sakamakon asusun gwamnatin na bai-daya da gwamnatin sa da kaddama wanda a da can kudaden suke shigewa asusun bankunan kasar nan.
Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba kasar ya bayyana hakan yayin bikin bayar da lambar yabo ga macancanta kawo ci gaban kasa a gwamnatin sa wadda ya hadar har da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya, Winifred Oyo-Ita.
KARANTA KUMA: Hadimin Shugaba Buhari ya mayar da martani ga Hadimin Jonathan
Shugaban kasar ya kuma bayyana cewa, tsare-tsaren da gwamnatin sa ta gindaya sun rage hauhawar farashi da kimanin kaso 12.5 cikin 100.
Ya kara da cewa, matsin tattali arziki da kasar nan ta afka a shekarar 2016 da ta gabata a sakamakon dogaro da man fetur da kuma wawuson asusun gwamnati babu sassauci.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng