Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO

Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO

Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya karbo bakuncin mambobin kungiyar magoya bayansa wato Buhari Support Organization BSO a yau Talata, 22 ga watan Mayu, 2018 a fadar shugaban kasa da ke Aso VIlla, Abuja.

Mambobin wadanda suka kawo ziyara karkashin jagorancin babban kwantrolan hukumar kwastam, Kanal Hamid Ali (mai murabus) da shugaban hukumar UBC, Dakta Mahmud Abubakar.

Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO
Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO

Shugaba Buhari ya zafafan magana yayin tattaunawarsa da kungiyar BSO. Ya bayyana yadda ya je babban bankin tarayya CBN ya tambayi cewa nawa muke dashi a asusu, amma gwamnan bankin ya bayyana masa cewa babu komai cikin asusun Najeriya illa basussuka.

Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO
Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO

Kana ya basu hakurin kan rashin tuntubarsu kafin alanta niyyar takaransa a zaben 2019 a ranan 9 ga watan Afrilu a taron masu ruwa da tsakin jam'iyyar. Ya mika godiyarsa da goyon bayan da suka nuna masa a zaben 2015 da kuma yanzu da yake ofis.

KU KARANTA: Mun shirya tsaf don farfado da Jirgin saman Najeriya nan da ‘yan watanni – Gwamnatin tarayya

Mambobin sun jaddada goyon bayansu ga shugaba Buhari kuma su da yan mafi yawancin yan Najeriya na shirye daram dam da sake neman takararsa.

Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO
Hotunan ganawar shugaba Buhari da mambobin kungiyar magoya bayansa BSO

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel