Karfin shari’a: Wani Mutumi ya yi barazanar kashe makwabcinsa, ya ɗanɗana kuɗarsa

Karfin shari’a: Wani Mutumi ya yi barazanar kashe makwabcinsa, ya ɗanɗana kuɗarsa

Jami’an rundunar Yansandan babban birnin tarayya Abuja, sun gurfanar da wani mutumi mai shekaru 32, Expert Jazhi gaban kuliya manta sabo biyo bayan barazanar kashe makwabciyarsa da yayi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Jazhi wanda mazauni ne a unguwar Jikwoyi dake Abuja, yana fuskantar tuhumar guda daya biyo bayan barazanar kashe makwabciyarsa Nkem Anikwe da ya yi.

KU KARANTA: Karamar magana ta zama babba: An hallaka wani Musulmi saboda ya yanka Saniya

Dansanda mai kara, Edwin Ochayi ya bayyana ma Kotun cewa Anikwe ta kai musu karar Jazhi a ofishin Yansanda dake Karu, a ranar 25 ga watan Afrilu, inda ta ce a ranar 9 ga watan Afrilu ne Jazhi ya yi barazanar kasheta.

Dansanda Ochayi ya bayyana cewa yin barazanar kashe wani ba tare da hakki ba ya saba ma sashi na 397 na kundin hukunta manyan laifuka, sai dai nan take Jazhi ya yi caraf ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa akai.

Bayan suararon dukkanin bangarorin ne sai Alkalin Kotun mai sharia Hassan Ishaq ya bada belin Jazhi akan kudi naira dubu dari biyu, (200,000) tare da mutum guda da zai tsaya masa akan kudi N200,000 shi ma.

Daga karshe Alkali Hassan ya umarci wanda ake kara da mai kara dasu rubuta yarjejeniyar zaman lafiya, tare da bada tabbacin tabbatar da bin doka da ka’ida a unguwanninsu har zuwa ranar 28 ga watan Yuni da za’a cigaba da sauraron karar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel