Badakalar naira miliyan 500: Kotu ta daure yaron tsohon shugaban kasa Shehu Shagari

Badakalar naira miliyan 500: Kotu ta daure yaron tsohon shugaban kasa Shehu Shagari

Wata babbar Kotun tarayya dake zamanta a garin Sakkwato ta yanke hukunci daure wani tsohon Minista kuma yaron tsohon shugaban kasa Usman Shehu Shagari biyo bayan kararsa da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta shigar da shi.

Legit.ng ta ruwaito a ranar Talata, ga watan Mayu ne aka fara sauraron karar da EFCC ta shigar da Shagari, tsohon kwamishinan watsa labaru na jihar, Ibrahim Gidado, kanin tsohon gwamnan jihar Sakkwato Attahiru Bafarawa, Nasiru Bafarawa, tsohon dan takarar gwamna a PDP, Sanata Abdallah Wali da tsohon shugaban PDP na jihar Ibrahim Milgoma.

KU KARANTA: Ana tare: Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon gwamnan jihar Filato da Kotu ta daure shi a Kurkuku

EFCC na tuhumar mutanen ne da laifin yin watanda da wasu makudan kudade da suka kai naira miliyan dari biyar, wadanda suka fito daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man fetir, Diezani Madueke, da nufin su murda ma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Badakalar naira miliyan 500: Kotu ta daure yaron tsohon shugaban kasa Shehu Shagari
Mukhtar Shagari a Kotu

Lauyan EFCC ya bayyana cewa laifukan da ake tuhumar Shagari, Wali, Milgoma, Nasiru Bafarawa da Ibrahim Gidado ya saba ma sashi na 18 na kundin hukunta laiukan satar kudi, kuma hukuncisa na nan a sashi na 16 (2) na kundin.

Sai dai bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkalin Kotun Mai shari Saleh Kogo Idrissa ya bada umarnin a daure su duka a shelkwatar rundunar Yansandan jihar. Mai sharia Idrissa ya umarci a garkamesu har zuwa ranar 24 ga watan Mayu, inda zai saurari bukatarsu ta samun beli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel