Mahaifin budurwar da saurayinta ya kashe ya fadawa saurin nata cewa sai ya auri gawar diyar tasa
- Iyayen marigayiya Confidence Nwanma sun hakikance kan cewa saurayinta da ake zargi da kashe ta, dole ya auri gawar ta
- Iyayen nata sunyi ikirarin cewa wanda ake zargin Saliu ladayo, dole sai yayi abubuwan al’adun aure ga gawar diyar tasu
- Ladayo ya amsawa hukumar ‘Yan Sanda cewa shi ya kashe Nwanma a lokacin da suke fada a tsakaninsu
Iyayen marigayiya Confidence Nwanma, wadda saurayinta Saliu Ladayo, da daba mata wuka har lahira lokacin da suke fada tsakaninsu, sunyi ikirarin cewa ya zama dole ya auri gawar diyar tasu, kuma sai ya gabatar da duk al’adun da akeyi na aure.
Punch ta ruwaito cewa, Ladayo wanda ke hannun hukumar ‘Yan Sanda ya amsa laifinsa na cewa tabbas shi ya kashe Nwanma, lokacin da suke fada a gidansa dake unguwar Oshinle, a garin Akure, jihar Ondo.
Mahaifin marigayiyar Jude Nwanma, lokacin da yake magana da manema labarai a gidansa dake Oke Aro, Akure, yace ya zama dole Ladayo ya dauki gawar ‘yar tasu zuwa kauyensu dake karamar hukumar Oru a jihar Imo, an daura masu aure kafin a rufe gawar tata.
KU KARANTA KUMA: Wakilan majalisa zasu gana da shugaba Buhari a yau game da lamarin dake tsakanin Saraki da IGP
Jude Nwanma, ya bayyana cewa duk wasu al’adu da akeyi na aure sai yayi matasu da kuma danginta sannan zasu barshi ya tafi, idan kuma bah aka ba duk danginsa ba wanda zai kai shekarun diyarsa zai mutu shim aba zato ba tsammani kamar diyarsa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng