Gwamnatin tarayya ta zayyana jahohi 35 da za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana

Gwamnatin tarayya ta zayyana jahohi 35 da za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana

Jami'an hukumar gwamnatin tarayya dake da alhakin kula da harkokin ma'adanan ruwa da binciken su watau Nigeria Hydrological Services Agency, NIHSA a takaice a ranar Alhamis din da ta gabata sun zayyana cewa kananan hukumomi 380 ne a cikin jahohi 35 za su fuskancin ambaliyar ruwa a daminar bana.

Kamar dai yadda muka samu, hukumar ta Nigeria Hydrological Services Agency ta kuma bayyana cewa akalla kananan hukumomi 78 ne za su fuskanci matsalar ambaliyar sosai fiye da sauran.

Gwamnatin tarayya ta zayyana jahohi 35 da za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana
Gwamnatin tarayya ta zayyana jahohi 35 da za su fuskanci ambaliyar ruwa a daminar bana

KU KARANTA: Karuwai daga Najeriya sun bayyana yadda suke rayuwa a Turai

Legit.ng ta samu cewa tuni dai hukumar ta NIHSA suka ankarar da gwamnatocin da lamarin ya shafi da nufin tunkarar bala'in tare kuma da rage radadin da hakan zai haifar.

A wani labarin kuma, Babban malamin addinin kirista kuma shugaban 'yan darikar Katolika mazauna garin Abuja mai suna John Onaiyekan ya sha alwashin jagorantar dubun dubatar jama'a mabiyan sa domin yi wa shugaba Muhammadu Buhari zanga-zanga.

Kamar dai yadda ya shaidawa manema labarai, zanga-zangar da suka shirya yi wa Buhari din na da nasaba da yadda suka ce yayi wa harkar tsaron kasar rikon sakainar kashi a na kashe kiristoci musamman ma a shiyyar Arewa ta tsakiya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel