Kwankwaso zai lashe kujerar shugaban kasa idan ya dawo NUP - Opara

Kwankwaso zai lashe kujerar shugaban kasa idan ya dawo NUP - Opara

Shugaban jam'iyyar National Unity Party (NUP) na kasa, Cif Perry Opara, yace akwai yiwuwar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019 mutukar ya canja sheka zuwa jam'iyyar (NUP) din

Kwankwaso zai lashe kujerar shugaban kasa idan ya dawo NUP - Opara
Kwankwaso zai lashe kujerar shugaban kasa idan ya dawo NUP - Opara

Shugaban jam'iyyar National Unity Party (NUP) na kasa, Cif Perry Opara, yace akwai yiwuwar tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2019 mutukar ya canja sheka zuwa jam'iyyar (NUP) din.

DUBA WANNAN: Kungiyar APC Aqida na barazanar barin jam'iyyar APC

Opara wanda yayi magana a karshen satin nan a babban birnin tarayya Abuja, ya ce tura shugaban kasa Muhammadu Buhari ba karamin wahala zai yi ba a zaben shekara mai karatowa, amma da akwai yiwuwar mutane irin su Kwankwaso da al'umma ke kauna ya iya ture shugaba Buharin.

Shugaban jam'iyyar NUP din yace, za'a iya danka amanar kasar nan a hannun Kwankwaso, sannan kuma yana da tabbacin cewa zai kawo cigaba fiye da yanda mutane ke tunani, amma hakan ba zai yiwu ba har sai ya dawo jam'iyyar NUP sannan kuma ya zabi mataimaki nagari.

"Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana da masoya masu tarin yawa a arewacin Najeriya, amma shi Sanata Kwankwaso yana daya daga cikin 'yan siyasar da suke da masoya a ko ina a fadin kasar nan. Idan har Kwankwason yana son zama shugaban kasa a 2019 a karkashin jam'iyyar NUP, sannan kuma idan har zai amince ya dauki mataimakin sa daga kudancin Najeriya, musamman ma cikakken Kirista, wanda yasan ya kamata, to tabbas zai lashe kujerar shugaban kasa a 2019.

"Kwankwaso ba mutum ne mai yawan surutu ba, babu ruwan shi da shiga sabgar da ba tashi ba, aikin shi yafi surutun shi yawa, yana girmama matasa, sannan kuma yana tafiya da kowanne jinsi walau mace ko namiji," inji shi.

Opara yace duk wanda ya samu nasarar ture shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2019 to ba karamin jan gwarzo bane, inda yace "Mutane suna kaunar Buhari fiye da yanda suke son jam'iyyar APC, sannan kuma Buhari shine APC, idan babu shi to APC ta mutu."

Wasu daga cikin jiga-jigan Kwankwasiyya, sun halarci taron jam'iyyar ta NUP, wanda aka gabatar a babban birnin tarayya a ranar Larabar nan data gabata.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel