Soja ya halaka matarsa bayan ya gano dukkan yaran da ta haifa ba nasa ba ne

Soja ya halaka matarsa bayan ya gano dukkan yaran da ta haifa ba nasa ba ne

Wani soja a kasar Zambia mai suna Pathias Mwape ya halaka matarsa, Esther mai shekaru 33 bayan ya gano cewa ba shine ainihin mahaifin 'ya'ya ta haifa masa a zaman aurensu ba.

An gano cewa wani maigidansa a wajen aiki ne mahaifin yaran biyu.

Lamarin dai ya faru ne a barikin soja na Chindwin da ke Zambia inda marigayiyar matar ta rika soyaya da mai gidan mijin na ta.

Sojan dai ya ji tsegumi a gari ne inda ake cewa ba shine ainihim mahaifin yaransa ba, hakan yasa ya tirke matar tasa wacce jami'an 'Yar sanda ce kuma ta fashe da kuka inda ta tabbatar masa da cewa yaran ba nasa ba ne.

Soja ya halaka matarsa bayan ya gano dukkan yaran da ta haifa ba nasa ba ne
Soja ya halaka matarsa bayan ya gano dukkan yaran da ta haifa ba nasa ba ne

Hakan yasa Mwape ya bindige matar tasa har lahira kuma daga bisani ya kashe kansa bayan 'yan sanda sun fara neman sa ruwa a jallo.

Wani soja da ya yi tsokaci kan lamarin ya ce, "Labarin ya dade yana yawo a gari, duk da cewa sun dai sun sani cewa matar tana cin amanan mijinta da maigidansa. Hakan yasa mutane ke kyautata zaton yaran ba na mijin bane. Ransa ya baci sosai a safiyar da ya kashe matarsa, ya tafi neman maigidansa don ya harbeshi amma bai same shi ba.

KU KARANTA: An kwata: Mamba a majalisar wakilai ya bankado cushe a kasafin kudin bana

"A lokacin da mijin ya tafi aikin samar da zaman lafiya a shekarun baya, daya daga cikin manyan sojin yakan tafi ya kwana a gidan Mwape, kowa ya san labarin. Shugabanin sojin duk sun sani, muna jira mu ga matakin da za su dauka ne."

Wani soja a barikin Chindwin ya bayyana cewa dama manyan sojojin sun saba neman matan kananan soji a barakin.

Mahaifin marigayar, Moses Mulombwa wanda shima tsohon dan sanda ne ya shaidawa Times of Zambia cewa shi da diyar nasa sunyi hasashen cewa wani abu mai kaman haka yana iya faruwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng