‘Yan kungiyar addinin kirista na Katolika zasu fita zanga-zanga a ranar Talata, a birnin tarayya

‘Yan kungiyar addinin kirista na Katolika zasu fita zanga-zanga a ranar Talata, a birnin tarayya

- Mambobin kungiyar addinin kirista na Katolika dake birnin tarayya, zasu fita nuna rashin jin dadinsu game da rashin tsaro da kuma mulkin rashin adalci a Najeriya

- Labari yazo cewa zasu fara zanga-zangar ta lumana ne daga National Ecumenical Center, sannan kuma za’a kare a Our Lady Queen of Nigeria Catholic Church, dake Garki a birnin tarayya

- Labari ya kara zuwa cewa mabiya darikar Katolika a ko ina dake dake fadin Najeriya kungiyar ta bukaci su gudanar da irin wannan zanga-zangar a jihohin da suke

Mambobin kungiyar addinin kirista na Katolika, dake birnin tarayya, a ranar Talata, zasu fita nuna rashin jin dadinsu game da rashin tsaro da kuma mulkin rashin adalci a Najeriya.

Labari yazo cewa zasu fara zanga-zangar ta lumana ne daga National Ecumenical Center, sannan kuma za’a kare a Our Lady Queen of Nigeria Catholic Church, dake Garki a birnin tarayya.

‘Yan kungiyar addinin kirista na Katolika zasu fita zanga-zanga a ranar Talata, a birnin tarayya
‘Yan kungiyar addinin kirista na Katolika zasu fita zanga-zanga a ranar Talata, a birnin tarayya

Labari ya kara zuwa cewa mabiya darikar Katolika a ko ina dake dake fadin Najeriya kungiyar ta bukaci su gudanar da irin wannan zanga-zangar a jihohin da suke don jawo da hankalin gwamnati game da matsalolin dake damun kasar musamman na rashin tsaro.

Sakatare Janar na catholic Secretariat of Nigeria (CSN), Rev. Fr. Ralph Madu, yace za’a gudanar da zanga-zangar ne domin girmama manyan malaman darikar Catholic din wadanda aka kashe tare da wasu mutane a watan da ya gabata a jihar Binuwai, wanda wasu filani ‘yan ta’adda suka kashe.

KU KARANTA KUMA: Idan muka bi abunda Allah yace kasarmu zata canza - Osinbajo

Manyan malaman sune Rev. Fr. Joseph Gor da kuma Felix Tyolaha, tare da wasu mutane 17 wadanda aka kashe suna cikin gabatar da bautar safe lokacin da ‘yan ta’addan suka kai masu hari suka kashesu. Za’a rufesu a ranar Talata, a Sesugh Maria Pilgrimage centre, Ayati, dake jihar Binuwai.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng