Yanzu - Yanzu: 'Yan Sabuwar jam'iyyar nPDP sun kai ziyara APC hedkwatar
- 'Yan sabuwar jam'iyyar nPDP dake cikin jam'iyyar APC mai mulki sun kaiwa wata ziyara babbar hedkwatar jam'iyyar APC ta kasa don ganawa da shugabannin jam'iyyar a yau
- Tawagar wacce ta samu jagorantar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, sun gana da mataimakin jam'iyyar APC na kasa, Sanata Lawal Shu'aibu
'Yan sabuwar jam'iyyar nPDP dake cikin jam'iyyar APC mai mulki sun kaiwa wata ziyara babbar hedkwatar jam'iyyar APC ta kasa don ganawa da shugabannin jam'iyyar a yau. Tawagar wacce ta samu jagorantar tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Alhaji Abubakar Kawu Baraje, sun gana da mataimakin jam'iyyar APC na kasa, Sanata Lawal Shu'aibu.
DUBA WANNAN: Kar a yaudare ku da kudi wurin zabe - Oshiomhole
Sauran mambobin kwamitin taron na jam'iyyar APC sun hada: Sakataren jam'iyyar na kasa, Alhaji Mai Mala Buni, Sakataren shirye-shirye na kasa, Sanata Osita Izunaso, Shugaban matasan jam'iyya na kasa, Hon. Ibrahim Jalo Dasuki, sai kuma Alhaji Mohammed Bala Gwagwarwa.
Sabuwar jam'iyyar ta nPDP ta ziyarci sakatariyar jam'iyyar a makon daya gabata, inda ta bukaci ganawa da shugabannin jam'iyyar ta APC a cikin kwanaki bakwai.
A cikin wata takarda da kungiyar ta aika; inda ta bukaci mafita don magance matsalolin dake tsakanin ta da jam'iyyar ta APC, suka ce, "Bisa ga dalilin rashin lokaci da kuma karatowar babban taron jam'iyya, muna bukatar a gabatar da wannan taron cikin nan da kwanaki bakwai daga ranar da aka karbi wannan takardar."
Amma a cikin 'yan kwanakin nan, wani rukuni na nPDP din wanda Sanata Abdullahi Adamu ya jagoranta sun ware kansu daga cikin kungiyar, inda suka ce ba a tuntube su ba kuma zargin da ake yi a cikin takardar da Baraje ya aika ba gaskiya bane.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng