Hadimar Buhari tace Wike na bukatar ganin likitan mahaukata
- Lauretta Onochie, daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari tace Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers yana da matsalar kwakwalwa
- Onochie ta mayar da martini ga gwamnan akan maganar da yayi na cewa anyi amfani da karfin tarayya anci mutuncinsa a jiharsa
- Onochie a kafar sadarwa na tuwitta tace dokar kasa bazata canza ba akan yanda ta bawa kowane dan kasa damar nemarwa shugabansu maganin mahaukata
Lauretta Onochie, daya daga cikin hadiman shugaban kasa Muhammadu Buhari tace Nyesom Wike, gwamnan jihar Rivers yana da matsalar kwakwalwa
Onochie ta mayar da martini ga gwamnan akan maganar da yayi na cewa anyi amfani da karfin tarayya anci mutuncinsa a jiharsa.
Wike ya bayyana hakan ne a ranar litinin lokacin da yake zantawa da manema labarai na gidan Talabijin na Channels.
Wike yayi ikirarin cewa anyi amfani da hukumar yaki da rashawa wurin sanyawa al’amuran jihar ido, duk da dokar da kotu ta kafawa hukumar tun kafin hawansa kujerar ta gwamna, wanda a ganinsa takura ce.
KU KARANTA KUMA: Idan muka bi abunda Allah yace kasarmu zata canza - Osinbajo
Onochie a kafar sadarwa na tuwitta tace dokar kasa bazata canza ba akan yanda ta bawa kowane dan kasa damar nemarwa shugabansu maganin mahaukata.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng