Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Najeriya, duba ko garinku na ciki

Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Najeriya, duba ko garinku na ciki

- Damunar bana ta fara kankama, yau za'a sha ruwa kamar da bakin kwarya

- Wata hukuma dake da masaniya kan hasashen yanayi ce ta bayyana hakan

Hukumar lura yanayi t kasa (NiMet) tayi hasashen cewa za’a sha mamakon ruwan sama a yawancin biranen kasar nan a safiyar yau Litinin.

Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Njariya, duba ko garinku na ciki
Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Njariya, duba ko garinku na ciki

NiMet ta ce za’a yi tsawa akai-akai a wasu bangare na babban birnin tarayya Abuja da Kaduna, Benue, Nasarawa, Kogi, Kwara, Plateau, Taraba da kuma Yola.

Bayanin hakan ya fito ne daga babban ofishin hasashen hukumar na kasa dake Abuja a jiya Lahadi.

NiMet ta kuma hasaso cewa yanayin zafin garuruwan zai na hawa da sauka a matakin 32 zuwa 37 da 22 zuwa 28 a zuruftun ma’auni.

KU KARANTA: Idon wasu Malamai ya raina fata sakamakon gicciye wata daliba

Rahoton hasashen ya kuma kara da cewa da rana ma a kwai yiwuwar sake samun wani ruwan saman a garuruwan Plateau, Kaduna da Nasarawa.

Sannan kuma hasashen ya bayyana cewa duk jahohin kudancin kasar zasu fuskanci yanayin tsawa da Ruwan sama a safiyar ta yau. Kuma daga bisani yanayin zai sai-saita tsakanin 30 zuwa 33 da kuma 20 zuwa 24 a ma’aunin Celsius.

Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Njariya, duba ko garinku na ciki
Za’a tsula ruwan sama a yawancin Biranen Njariya, duba ko garinku na ciki

Haka zalika rahoton ya bayyana cewa jahohin Arewacin kasar nan daga safe zuwa dare yanayin zai na hawa da sauka bisa 34 zuwa 41 da kuma 23 zuwa 28. Kuma a cikin sa’o’in ranar (Litinin) za’a samu zubar Ruwa sosai kamar da bakin kwarya.

A don haka ga mai shirin fita sai ya nemi lema ko ya hanzarta fita domin samun maboya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng