Gwamnan jihar Borno ya fatattaki 'yan cacar Bet9ja daga jihar sa

Gwamnan jihar Borno ya fatattaki 'yan cacar Bet9ja daga jihar sa

Gwamnan jihar Borno dake a yankin Arewa maso gabashin kasar nan Alhaji Kashim Shettima ya sanar da bada umurnin fatattakar dukkan masu ruwa da tsaki da masu shirya cacar nan ta kwallo da wasanni ta NaijaBet a dukkan fadin jihar.

Gwamna Shettima dai ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabin sa a wajen taron karawa juna sani da hukumar gidan radio da talabijin na jihar wato BRTV ta shirya a karo na sha hudu a yau.

Gwamnan jihar Borno ya fatattaki 'yan cacar Bet9ja daga jihar sa
Gwamnan jihar Borno ya fatattaki 'yan cacar Bet9ja daga jihar sa

KU KARANTA: Babban malamin addini ya lekowa Buhari faduwa a 2019

Legit.ng ta samu kuma cewa al'ummar jihar ma dai da yawan su sun goyi bayan wannan mataki da Gwamnan dauka.

A wani labarin kuma, Yayin da musulmai a dukkan fadin duniya ke cigaba da azumtar azumin wata mai falala na Ramadana, tuni dai falalar watan ta fara ratsa zukatan wasu mutanen da da ma musulmai bane suna ta komawa musulmai cikin falalar ubangiji.

Mun samu cewa dai a irin hakan ne ma wata baiwar Allah mai suna Mercy da a da kirista ce ta karbi kalmar shahada sannan kuma ta zabi sunan A'ishatu a garin Yola, babban birnin jihar Adamawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel