Zaben 2019: Wani babban malamin addini ya lekowa Buhari rashin nasara

Zaben 2019: Wani babban malamin addini ya lekowa Buhari rashin nasara

Wani babban malamin addinin kirista kuma shugaban rukunin majami'un Divine Intelligence mai suna George Fakolade a ranar Asabar din da ta gabata ya gargadi shugaba Muhammadu Buhari akan takarar da yake yi na neman tazarce a zaben 2019 mai zuwa inda yace shi ya leko masa rashin nasara.

Babban malamin addinin na Kirista George Fakolade ya dai bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci ofishin jaridar Vanguard inda kuma ya ce tabbas idan har shugaban kasar bai dena ba to fa lallai akwai matsala babba.

Zaben 2019: Wani babban malamin addini ya lekowa Buhari rashin nasara
Zaben 2019: Wani babban malamin addini ya lekowa Buhari rashin nasara

KU KARANTA: Ana rigimar kan iyaka a tsakanin jahohi 2 a Arewa

Legit.ng ta samu cewa babban malamin haka zalika ya kuma bayyana cewa shi yawancin abunuwan da ya leko suna zama gaskiya don kuwa ya leko faduwar shugaba Jonathan zabe a 2015 da ma mutuwar marigayi shugaba Yar'aduna.

A wani labarin kuma, 'Yan Najeriya biyu yanzu haka kamar dai yadda labari ya iske mu dake zaune a babban birnin Landan dake a kasar Birtaniya bayan kotu ta same su da laifin yin damfara da kuma zamba cikin aminci ta zunzurutun kudin da suka kai Euro miliyan daya.

'Yan Najeriyan masu sunaye kamar haka Emmanuel Mmaduike da kuma Olawale Kashimawo wadanda dukkan su keda shekaru 31 a duniya an dai same su ne da laifin yin anfani da yanar gizo tare da karkatar da kudaden kamfanoni zuwa asusun ajiyar su.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng