Masu amfani da kafafen sadarwa fiye da kima na da tabin hankali - Sabon bincike

Masu amfani da kafafen sadarwa fiye da kima na da tabin hankali - Sabon bincike

- Jaridar The Economist ce ta fitar da bayanan masu nuna akwai masu matsala a al'uma

- Su dai masu amfani da yada sadarwa ta zamani basu ma san ko akwai illa ba ko babu

- Samari da 'yan mata sunfi kowa nacin son wannan al'ada ta soshiyal midiya

Masu amfani da kafafen sadarwa fiye da kima na da tabin hankali - Sabon bincike
Masu amfani da kafafen sadarwa fiye da kima na da tabin hankali - Sabon bincike

Jaddawali da alkalumma da masana suka fitar sun alakanta tabin hankali da yawan makalewa a sashen soshiyal midiya na sadarwa ta zamani, inda akan ga wasu sun ki barin online dindin-din.

A sabon binciken, masana sunce akwai yiwuwar wadanda ke makale wa facebook da iri-irensa suna da matsala ne ko ta abota ko ta tabin hankali.

Kadaici, da son ayi dani da ma zullumi watau depression, su ke damun da yawa daga matasa a wannan zamani, sai dai ba'a farga sai abin ya kai la-haula.

DUBA WANNAN: Shugaban Amurka daqiqi ne - Gates

Rashin more wa rayuwa ta gaske, kamar yawo, shakatawa, abokai na gaske, shan iska a yammaci a waje, fira, soyayya, abokai, bacci isasshe da ma raha, sune maganin irin wannan kadaici da intanet ke haifarwa a zamanin nan.

Shi dai zullumi yana samun mutane da yawa, wanda daga baya sai su koma ko shaye-shaye ko su janye daga mutane, wasu lokutan sai ma su zama wasu ababen daban, kamar hauka tuburan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel