Sojin Najeriya sun kadar da wasu mahara da niyyar kunar bakin wake a Borno dazunnan

Sojin Najeriya sun kadar da wasu mahara da niyyar kunar bakin wake a Borno dazunnan

- Maharan sun so kai hari kan masu azumi ne a Kawuri

- Sanarwar hukumar sojin ta nunna maharan su biyu ne

- Ana kan kokarin sulhu da Boko HAram masu jihadi kan jama'a

Sojin Najeriya sun kadar da wasu mahara da niyyar kunar bakin wake a Borno dazunnan
Sojin Najeriya sun kadar da wasu mahara da niyyar kunar bakin wake a Borno dazunnan

Sanarwar da Sani Kuka Sheka ya fitar a yau a shafinsa na Facebook ta nuna sojin dake aikin Operation Lafiya Dole ta nuna cewa soji sun kare wani hari da masu kunar bakin wake suka so kaiwa kan sojoji ko jama'ar garin Kawuri.

'Yan matan biyu an dauro musu bom ne cewa su je suyi 'aikin Allah'. Sai dai da tsakar daren jiya da suka lababo zasu kai hari kan sojojin, sai dai an tsaida su tun daga nesa suka ki tsayawa, sai kawai sojin suka dauke su.

DUBA WANNAN: Ebola tafi karfin WHO ya zuwa yanzu

Bam din daya ya fashe inda ya kashe su 'yan matan su biyi, amma na daya bai fashe ba.

Boko Haram dai sun dage wai sai sun kafa daular Islama sun kori hukuma da gwamnatin Najeriya, jahilci da har yanzu ya gagara yiwuwar musu kuma yana sanya su asarar jama'a da iyalansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng