Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Wata kungiyar kwararrun likitoci ta samu nasarar raba wasu tagwayen jarirai mata a cibiyar lafiya ta birnin Yola dake jihar Adamawa.

Jagoran wannan kwararrun likitoci, shugaban cibiyar lafiyan, Farfesa Auwal Abubakar, shine ya bayyana hakan yayin ganawar sa ta ranar Juma'a da manema labarai a birnin Yola.

Farfesa Auwal yake cewa, sun samu nasarar raba wannan jarirai biyu da aka haife su a manne da juna.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an gudanar da wannan aiki na tiyata a ranar 14 ga watan Mayu, inda kwararrun likitocin suke kyakkyawan zato akan ci gaba da dorewar rayuwar su cikin koshin lafiya sakamakon ingancin nasara da suka samu yayin aikin.

Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola
Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola
Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola
Likitoci sun raba wasu Tagwaye da aka haifa manne da juna a birnin Yola

Babban likitan ya bayyana cewa, sun samu nasarar kammala wannan aiki ne cikin sa'o'i hudu na gudanar da tiyata.

KARANTA KUMA: Rikicin Jam'iyya: Dogara da wasu Mutane 9 sun yi korafin Oyegun har Gaban Kuliya

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan shine karo na biyu da aka gudanar da makamancin wannan aiki a asibitin.

Daga karshe babban likitan ya kara da cewa, wannan shi yake tabbatar da kwarewar likitoci a kasar nan ta yadda za su iya gogayya da abokan aikin su dake kasashen da suka dara kasar Najeriya ta fuskar ci gaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng