'Fadan addini na iya ballewa muddin yarinyar Dapchi Leah ta mutu a hannunn Boko Haram'
- Kungiyar nan ta kiristoci ta Nageriya wato CAN tace matukar Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram akwai yiwuwar yaki tsakanin addinan
- Leah Sharibu dai Itace yarinya guda daya data rage a hannun Boko Haram daga cikin dalibai 112 na Dapchi da sukayi garkuwa dasu
- Boko Haram taki sakin Sharibu ne saboda taki barin addinin kirista
CAN:Matukar Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram to fa hakan zai janyo yaki tsakanin addinai a Nageriya.
Kungiyar nan ta kiristoci ta Nageriya wadda akafi sani da CAN tace matukar Leah Sharibu ta mutu a hannun Boko Haram to fa hakan zai janyo afkuwar yaki a tsakanin addinai.
Sharibu wadda a ranar Litinin taka shekaru 15 Itace kadai ta rage a hannun Boko Haram daga cikin dalibai 112 da sukayi garkuwa dasu a garin Dapchi jahar Yobe 19 ga watan Febrairu daya gabata.
Duk da cewa da yawa daga cikin yaran sun sake samun yanci amma banda Sharibu a bisa bijirewa da tayi taki barin addinin kirista.
A bisa ruwayar PUNCH Adebayo Oladeji mataimaki na musamman a bangaren yada labarai yace shugaban na CAN yace akwai rikici a Nageriya matukar Sharibu ta rasa ranta.
DUBA WANNAN: Najeriya zata gwada amfani da makamashin nukiliya
Oladeji yace "CAN bazata daina bibiya akan a saki wadanda aka kamaba ciki kuwa harda Leah Sharibu. Zamu miki tsaye akan hukumomin tsaro Sannan ya kamata Shugaban kasa Muhammad Buhari ya farka da bacci tun kafin yan ta'adda da makiyaya su kawo karshen kasar.
"Leah Sharibu bazata mutu ba, mutuwar ta zata kawo rikici a Nageriya domin kuwa kamar wani katin gayyata ne akan yaki tsakanin addinai. Saboda Leah ta tsaya tsayin Daka akan addinin ta."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng