Tantamar wai ko Adolf Hitler ya mutu a yakin duniya II, ko tsere wa yayi Argentina - Sabon Rahoto

Tantamar wai ko Adolf Hitler ya mutu a yakin duniya II, ko tsere wa yayi Argentina - Sabon Rahoto

- An tsammanin Hitler ya kashe kansa shi da Eva Braun matarsa da ya aura a ranar

- Wasu sabbin bayanai na nuna kamar dai wasu aka ajje a matsayin gawarsa, shi ya tsere zuwa Argentina

- Yanzu sabbin bayanaii sun sake tabbatar da lalle ya mutu a 1945 ba a 1975 ba

Tantamar wai ko Adolf Hitler ya mutu a yakin duniya II, ko tsere wa yayi Argentina - Sabon Rahoto
Tantamar wai ko Adolf Hitler ya mutu a yakin duniya II, ko tsere wa yayi Argentina - Sabon Rahoto

Babban ja'iri da ya azabtar da sunniya ya tsunduma ta cikin yakin da ya hallaka akalla mutum 100m da ruguza yawancin kasashen Turai, Adolf Hitler, ya mutu a 1945 ne a Berlin, ba a 1975 ba a Argentina kamar yadda wasu ke yadawa, fadin sabon bincike.

Masu binciken, na Faransa, sun sami kokon kansa ne da hakoran da aka adana a Moscow, babban birnin kasar Rasha, wadda ita ta fara isa ga gidan nasa na karkashin kasa a Berlin, inda ya kashe kansa da matarsa Eva.

DUBA WANNAN: Saurayi na yayi min ciki, a'a ni mijinta ni nayi

A baya dai, wasu na zargin lallai ya tsere ne ba wai kashe kansa yayi ba, inda wasu ke ganin yaje Argentina ne inda abokinsa ke murkin kama karya.

An saki wasu hotuna dake nuna wai har ya tsufa ya kai 1975 a raye, shekaru 30 bayan mutuwarsa ta asali.

Yanzu dai ta tabbata ya mutu, kuma gawarsa da aka kona ta bar burbushi da aka ajje a gidan tarihi a USSR.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng