Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria

Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria

Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa wani abu mai kama da tashin bam ya tashi a gefen gidan ruwan dake gadar Kwangila Zaria.

Sai dai a lokacin da jama’a suka bazama zuwa wajen domin ganin abunda ya afku sai suka ga ashe tukunyar gas ne ya fashe.

Hakan yayi sanadiyar mutuwar mai zuba gas din da ake kira da suna Jamilu mai gas sakamakon fata-fata da gas din ta yi da shi. Hakazalika shima wanda ake zubawa gas din ya mutu.

Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria
Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria

Fashewar tukunyar bai tsaya nan ba sai da ya tsallaka titi ya fadawa wani Mai Lemu da baro fuska. Da abin gas din ya yi sama sai da ya tayar da wuta a saman poll din da ke wurin. Abin na fadowa sai ya tartsu a jikin wata Mota inda ya farfasa gilas din bayanta.

Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria
Mummunan hatsarin gas ya kashe mutane 2 tare da jikkata wasu a Zaria

KU KARANTA KUMA: ‘Yan sanda sun gano N22m na bogi a jihar Gombe

Naman mutane haka kake gani a kasa, saboda akwai wadanda cikin su da cinyoyin su ya farfashe. A karshe dai mun samu tabbacin mutuwar mutane biyu inda mutum uku ke cikin mawuyacin hali.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel