Kungiyar Miyetti Allah ta kai karar wani gwamna gaban shugaba Buhari

Kungiyar Miyetti Allah ta kai karar wani gwamna gaban shugaba Buhari

- Kungiyar Miyetti Allah ta rubuta wasika ga shugaba Muhammadu Buhari don kokawa a kan dokar hana kiwo a Jihar Benue

- Kungiyar ta ce ba za ta amince da dokar ba hakan yasa ta maka gwamna Ortom a kotu

Shugabanin kungiyar makiyaya na Miyetti Allah sunyi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya ja kunnen gwamna Samuel Ortom na jihar Benue a kan batun dokar hana kiwo.

Kungiyar ta ce ba za ta amince da dokar hana kiwo da gwamnatin jihar ta kafa ba inda suka ce makiyaya suna da damar ziyarar jihohi da kuma yada zango a kowacce jiha kamar yadda sauran yan Najeriya ke dashi.

Kungiyar Miyetti Allah ta kai karar wani gwamna gaban shugaba Buhari
Kungiyar Miyetti Allah ta kai karar wani gwamna gaban shugaba Buhari

KU KARANTA: Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun canja sheka zuwa jam'iyyar SDP a jihar Jigawa

Jaridar Tribune ta ruwaito cewa wannan sakon na dauke ne cikin wata sanarwan bayan taro mai dauke da sa hannun Ciyaman din kungiyar, Alh. Abdullahi Bello Bodejor da sakatarensa, Injiniya Saleh Alhassan da kuma jami'in yadda labarai Garus Gidado.

Wani sashi na cikin sakon ya ce: "Muna Allah-wadai da ayyukan wasu kungiyoyi karkashin jagorancin wani Ariyo Atoye wanda suke yawa a garin Abuja suna bata wa makiyaya suna don su samu kudi wajen yan siyasa.

"Muna kira da Alkalin Alkalai na kasa yayi watsi da kiraye-kirayensu saboda gwamna Ortom wanda ya yi kaurin suna wajen daukan nauyin yan baranda don musgunawa Fulani makiyaya a jihar," inji sanarwan.

Kungiyar kuma tayi kira ga majalisar tarayya ta sanya baki cikin batun haramtawa wa jihar cigaba da amfani da dokar hana kiwon.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164