Jiragen ruwa guda 31 makare da man fetir da kayan abinci da takin zamani sun tinkaro Najeriya
Akalla manyan jiragen ruwa guda 31 da daya ne ake sa ran zasu fara isowa Najeriya ranar Juma’a 18 ga watan Mayu dauke da man fetir da sauran kayayyakin amfani, kamar yadda kamfanin dillancin labaru Najeriya, NAN, ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa, NPA ce ta sanar da isowar wadannan jiragen dankaro, inda tace ana sa ran jiragen zasu fara sauka ne tun daga ranar Juma’a 18 ga watan Mayu zuwa ranar Lahadi, 27 ga watan Mayu.
KU KARANTA: Wasu zakakuran likitoci a jihar Adamawa sun raba wasu jarirai 2 da suka zo Duniya a hade
NPA ta kara da cewa jirage guda 10 daga cikin 31 na dauke ne da tataccen man fetir, yayin da sauran guda 21 ke dauke da takin zamani, fulawa, danyen kifi, gishiri, sundukai da kuma wasu kayan amfani na daban.
Zuwa yanzu haka jirage guda takwas sun iso tashar jirgin ruwa na Apapa dake jihar Legas, inda suke jiran fara saukar da buhunan takin zamani, man fetir da bakin mai.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng