Sanata Shehu Sani ya bayyana abubuwa 15 da ke barazana ga damokradiyar Najeriya (jerin su)

Sanata Shehu Sani ya bayyana abubuwa 15 da ke barazana ga damokradiyar Najeriya (jerin su)

- Sanata Shehu Sani ya bayyana matsaloli 15 dake barazana ga siyasar Najeriya

- Dan majalisar na jihar Kaduna ya bayyana a shafinsa na Facebook matsalolin da yake ganinn sun shafi siyasar Najeriya

Sanata Shehu Sani ya bayyana matsaloli 15 dake barazana ga siyasar Najeriya.

Dan majalisar mai wakiltar jihar Kaduna ta tsakiya ya bayyana a shafinsa na Facebook matsalolin da yake ganinn sun shafi siyasar Najeriya.

Sanata Shehu Sani ya bayyana abubuwa 15 da ke barazana ga damokradiyar Najeriya (jerin su)
Sanata Shehu Sani ya bayyana abubuwa 15 da ke barazana ga damokradiyar Najeriya (jerin su)

1. Yawan kashe kashe a arewa ta tsakiya da kuma arewa ta yammacin Najeriya.

2. Karin yawan hare-hare da ake kaiwa a arewa maso gabashin Najeriya da kuma garkuwa da mutane da akeyi.

3. Hana muatane ‘yancin bayyana ra’ayoyinsu game da siyasa da kuma hana al’umma gabatar da zanga-zangar lumana.

KU KARANTA KUMA: Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger Gidauniyar Dangote ta tallafa wa mata da naira miliyan 250 a Jihar Niger

4. Nuna bambanci a tsakanin shuwagabanni da kuma wadanda suke mulki a matsayin abokan adawa.

5. Nuna bambancin addini da kuma kabilanci a tsakanin al’ummar Najeriya.

6. Rashin girmama umurnin kotu da kuma kin amincewa da doka game da abubuwan da suka shafi siyasa.

7. Rashin nuna kulawa ga al’umma da kuma nuna alfarma.

8. Rashin fahimtar juna a tsakanin jam’iyya mai mulki da kuma rashin tsari a al’amuransu.

9. Rashin tabbaci ga shuwagabannin majalisa masu wakiltar al’umma game da lamarin da ya shafi rashawa.

10. Rashin iya aiki da kuma kasakantar da hukumomin jami’an tsaro na kasar nan.

11. Rashin kula ga kungiyoyin jama’a da kuma na matasa.

12. Nuna son kai a fannin binciken wadanda suka aikata rashawa da cin hanci.

13. Rashin sanin ya kamata a majalisun jihohi da kuma gwamnoni masu tafiyar da al’amuransu ba tare da tsoron doka ba.

14. Hukunta masu zantuttuka na nuna kiyayya ga shugabannin gwamnatin, wanda hakan ke kare shuwagabannin suna aikata abunda suka ga dama akan talakawa.

15. Fifita bukatar shuwagabannin siyasa fiye da kwanciyar hankali da kuma zaman lafiyar mutanen Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel