Cakwakiya: wata gada ta rufta da wani Gwamna da mataimakinsa yayin da suke daukar hoton ‘Selfie’
Wai! Bahaushe ya yi gaskiya da yace ‘Bakauye ya yi agogo kowani layi sai daga hannu’, kusan abinda ya faru kenan a kasar Kenya, inda wani Gwamnan daya daga cikin jihohin kasar, Alfred Muta tare da mataimakinsa Joash Maangi suka afka cikin wani tafki.
Jaridar The Cables ta ruwaito gwamnan da mataimakinsa sun saki baki basu Ankara ba sai jin kansu suka yi tsundum cikin ruwan, a daidai lokacin da suke daukar hoton kai da kai, wanda ake kira da suna ‘Selfie’.
KU KARANTA: Dandalin Kannywood: Hadiza Gabon ta yi ma wasu gajiyayyu sha tara na arziki
Majiyar Legit.ng ta ruwaito abinka da manyan jami’an gwamnati, nan da nan masu gadinsu suka fanjama cikin ruwan, suka ceto rayuwarsu, inda suka garzaya dasu asibitin Ogembo dake lardin Kisii, sun jike sharkaf.
Wannan lamari ya faru ne awanni kadan bayan da jama’an kasar suka soki gwamnan da yawace yawacen bude ido yayin da wata gada a jiharsa ta tsatstsage, tana shirin karyewa.
Kaakakin lardin Kisii, Maseme Machuka ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai ya musanta rahoton cewa suna daukar hoto ne abin ya faru, inda yace: “Gwamnan da mataimakinsa sun fada cikin ruwa ne sakamakon gadar ta tsufa, amma basu samu rauni ba.”
Sai dai yayin da Machuka ke musanta wannan zargi, wani kamfanin jaridar, Capital News ta tabbatar da cewa gwamnan da mataimakin nasa suna daukar hoto ne a lokacin da lamarin ya faru, inda tace a gaban wasu ma’aikatanta guda biyu lamarin ya faru.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng