Masoyina yayi min ciki - wata matar aure, karya take ni nayi cikin - mijinta

Masoyina yayi min ciki - wata matar aure, karya take ni nayi cikin - mijinta

Wata mai siyarda biredi, Marian Folarin, a ranar Alhamis ta sanar da wata kotu a Mapo a jihar Ibadan cewa masoyin ta ne yayi mata ciki, ba mijin ta ba, Kayode Folarin.

Masoyina yayi min ciki - wata matar aure, karya take ni nayi cikin - mijinta
Masoyina yayi min ciki - wata matar aure, karya take ni nayi cikin - mijinta

Matar auren, mai yara hudu ta kawo karar mijinta ne a zargin shi da takeyi na rashin daukar dawainiyar da ta hau kanshi ta bangaren cikin gida.

Tace "Mai shari'a, yunwa, qishi da talauci sune abokan rayuwar mu a gidan Kayode kusan shekaru 20 da suka wuce. A da munyi yarjejeniya da Kayode cewa bazamu haifa yara sama da hudu ba kuma yayi kokarin ganin ya kare yarjejeniyar."

"Amma ya kasa kula da ni da yaran, bayan dukana da yake yi a koda yaushe. Na hana Kayode kwanciyar aure dani tun shekarar 2007 saboda kada in samu ciki. A yanzu maganar da nake, masoyina ne, Ololade, shi yayi min ciki."

"Ina rokon kotun nan mai alfarma da ta hana Kayode tsangwama ta da hantara ta. Saboda yanzu ni bani da ra'ayin auren shi yanzu. Na samu sabuwar soyayya."

Wanda ake zargi ya musanta duk zargin da ake mishi, kuma har yanzu yana son matar shi.

"Marian mashahuriyar makaryaciya ce, tana samun soyayyata da kulawa kuma mutane shaida na ne. Abin haushi ne ace, wasu na zigata. Mai shari'a, inaso in tabbatar maka cewa ni nayi mata ciki ba wani bakanike ba."

DUBA WANNAN: Kashe-kashen da ake ba na kabilanci ko addinanci bane

Diyar Marian yar shekara 14,ta bada shaidar Cewa babanta mutum ne mai kula wanda yake komai don yaga ya biya mana bukatunmu. Ina tunanin dai mahaifiyata bata da godiya ne. "

Mai shari'a Ademola Odunade ya bada izinin ayi ma Marian gwaji, a gane watannin cikin ta. Kuma masoyinta ya bayyana a gaban kotun a ranar 23 ga watan Mayu, inda za a cigaba da sauraron qarar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng