Birnin Gwari: Rayuka 8 sun salwanta a wani Hari na Sanyin Safiya
Kimanin rayuka 8 ne suka salwanta a wani sabon hari da ya afku da sanyin safiya a gundumar Kakangi dake karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.
Rahotanni da sanadin shafin jaridar Daily Trust sun bayyana cewa, wannan hari ya afku ne da misalin karfe 4:30 na Asubahin ranar Alhamis din da ta gabata a kauyukan Mashigi, Dokoru da Sabon Wuri.
Maharan sun kuma yi awon gaba da shanu da dama da kuma baburan hawa sama da goma yayin wannan hari.
Alhaji Ja'afar Jibril, wani mazaunin daya daga cikin wannan yankuna ya bayyana cewa, rayukan mutane hudu ne suka salwanta a kauyen Mashigi, yayin da biyu-biyu daga kowane kauyukan Dokaru da Sabon Wuri suka riga mu gidan gaskiya.
Mazaunin ya koken cewa, ya kamata gwamnatin jiha da ta tarayya ta kawo masu dauki da zai kwantar masu da lafiya sakamakon zaman dar-dar da suke yi.
KARANTA KUMA: Fadar Shugaban Kasar ta yi karin haske kan Bidiyon da ya bayyana Sufeto Janar na 'Yan sanda na Kakarin Magana a jihar Kano
Alhaji Ja'afaru ya kuma fadakar da wasu mutane dake bayar da rahotanni na karya da shaci fadi dangane da hare-haren dake afkuwa a yankin.
A yayin tuntubar kakakin 'yan sanda na jihar, ASP Mukhtar Aliyu ya tabbatar da afkuwar wannan hari, inda yace jami'an tsaro tuni suka bayyana a yankin domin fuskantar lamarin.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng