Aliko Dangote, Halima Dangote da surukinsa sun ziyarci Babangida a Minna
Fitaccen attajirin nan, Alhaji Aliko Dangote ya kai ma tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ziyara a gidansa dake saman Dutse a garin Minna na jihar Neja a ranar Alhamis, 17 ga watan Mayu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dangote ya samu rakiyar diyarsa, Hajiya Halima Dangote, mijinta Alhaji Suleiman Bello da sauran shuwagabannin kamfanin Dangote.
KU KARANTA: Ana nan dai jiya Iyau: Gungun yan bindiga sun far ma kauyukan Birgin Gwari guda 4
Dangote dai ya je jihar Neja ne domin wani bikin kaddamar da raba jari da gidauniyarsa ta baiwa mata masu karamin karfi, jarin da ya kai naira miliyan dari biyu da hamsin, N250m, kuma an raba shi ne ga mata dubu ashirin da biyar.
Bayan an kammala bikin raba kudaden ne, sai Dangote yayi haramar zarcewa gidan tsohon shugaban kasar, inda daga cikin tawagarsa har da gwamnan jihar, Abubakar Bello, Sanata Bala Ibn NaAllah, da shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Neja.
Isarsa keda wuya, aka yi masa iso, inda bayan gaisawa da IBB a bainar jama’a, aka shigar da shi wani daki, inda suka kulle kofa, suka kuma kwashe tsawon lokaci suna tattaunawa fiye da awa guda.
Sai dai Attajiri Aliko Dangote yayi gum da bakinsa, bai cewa yan jarida uffan ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng