Yadda aka koma amfani da kwanson alburusai domin kera zobe a Maiduguri (Hotuna)
Garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ya sha fama da matsalolin tsaro daga mayakan kungiyar Boko Haram tun shekarar 2009.
A lokacin da Boko Haram ke cin Karen su babu babbaka, tashin bama-bamai da jin harbe-harben bindigu ba wani bakon abu bane.
Wani ma’abocin amfani da dandalin da sada zumunta na Facebook, Mohammed Chiroma, ya ziyarci garin Maiduguri domin fadakar da jama’a a kan illolin sinadarai masu fashewa amma abin mamaki sai ya samu jama’ar garin na amfani da gyauron kayan yaki domin yin kwalliya.
DUBA WANNAN: Butai ya ziyarci Buhari, ya yi masa bayanin halin da tsaron kasa ke ciki (hotuna)
A cewar sa, “mun je wani kauye a Maiduguri domin yin wani aiki, amma abin lokacin da suka ga hotunan wasu kayan yaki masu hatsari, ciki hard a alburusai, sai suka ce, “muna amfani da kwanson alburusai domin kera zoben kwalliya,” kuma har ma wasu samari uku suka nuna min irin zobunan a hannayen su.
A wani labarin na Legit.ng a yau, kun ji cewar a kalla mutane hudu ne suka mutu a yau, Alhamis, bayan wani dan kunar bakin wake ya kai hari a wani masallaci dake sansanin ‘yan gudun hijira kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito.
Dan kunar bakin wake ya saje ne cikin masu ibada tare da tashin bam din dake jikin sa a wani sansanin ‘yan gudun hijira dake garin Dikwa mai nisan kilomita 90 a gabashin Maiduguri.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng