Malami ya sanyawa yarinya ‘yar shekara 6, fensiri a matancinta ya kuma goge jinin da ya fita daga jikinta da tsumman goge fuska
- Wani malami dan shakara 36 Lilian Ahaneku, a ranar Alhamis, ya gurfana a gaban kotun Ikeja, bisa zargin sanyawa yarinya mai shekaru shida fensira guda uku a gabanta
- Ahaneku wanda ke zama a 6, Alhaji Gudus Giwa St., Eyita, Ikorodu, a jihar Legas, yana fuskantar laifin cin zarafin dan adam a gaban kotun
- Mai gabatar da kara Christopher John ya fadawa kotun cewa wanda ake zargin ya kira yarinyar zuwa wani aji da babu kowa a ciki inda yak eta mata haddi
Wani malami dan shakara 36 Lilian Ahaneku, a ranar Alhamis, ya gurfana a gaban kotun Ikeja, bisa zargin sanyawa yarinya mai shekaru shida fensira guda uku a gabanta.
Ahaneku wanda ke zama a 6, Alhaji Gudus Giwa St., Eyita, Ikorodu, a jihar Legas, yana fuskantar laifin cin zarafin dan adam a gaban kotun.
Mai gabatar da kara Christopher John, ya bayyanawa kotun cewa an aikata laifin a ranar 24 ga watan Afirilu, a cikin harabar makarantar Zion Saint Nursery and Primary dake a No. 70, Ijokoro St., Ikorodu, a jihar Legas.
John ya fadawa kotun cewa wanda ake zargin ya kira yarinyar zuwa wani aji da babu kowa a ciki lokacin da ake gudanar da al’amuran makarantar, inda ya keta mata haddi.
KU KARANTA KUMA: Kotu ta daga shari’ar Sanata Dino Melaye har sai baba ya gani
Alkalin kotun mr. P.E Nwaka, ya bayar da wanda ake zargin akan belin kudi na N200,000 tare da mutane biyu da zasu tsaya masa, ya kuma daga shari’ar zuwa 13 ga watan Yuni, bayan yaki amincewa da laifin da ake zargin nasa da aikatawa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng