'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar

'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar

Rahotanni daga shafin Daily Post sun bayyana cewa, a ranar Larabar da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka tarwatsa wani taro na jam'iyyar APC yayin gudanar da shi a karamar hukumar Yakurr ya jihar Cross River dake kudancin Najeriya.

Majiyar rahoton kamar yadda jaridar ta bayyana ta bayyana cewa, 'yan bindigan sun tarwatsa taron jam'iyyar ne ta hanyar bude wuata ta harsashai da suka rinka asarar su a saman iska na sararin samaniya.

Mista Ibor, wani mashaidin wannan lamari na firgici da ya labartawa manema labarai ya bayyana cewa, a yayin da 'yan bindigar ke faman wannan razani ga al'umma sun kuma rinka kururuwa da yekuwar 'ba bu Minista ba bu taron jam'iyya'.

'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar
'Yan Bindiga sun tarwatsa taron jam'iyyar APC a Garin Calabar

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan lamari ya tilasta kwamitin masu ruwa da tsakin wajen daga ranar gudanar da taron jam'iyyar zuwa wani lokaci na gaba.

KARANTA KUMA: Tsawon Rayuwata Ukuba ce daga Ubangiji - Inji wata Tsohuwa mai shekaru 128 a Duniya

Shugaban karamar hukumar ta Yakurr, Mista Owan Kennethe, ya tabbatar da afkuwar wannan lamari, inda 'yan bindigan suka kai hari na ruwan duwatsu ga ofishin 'yan sanda na rukunin da ya janyo asarar dukiya ta wani munzali.

Kamar yadda shafin jaridar ta Daily Post ya ruwaito, wannan karamar hukuma ta Yakurr ita ce mahaifa ta Ministan Neja Delta, Usani Uguru Usani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel