Wani Matashi 'Dan Shekara 25 ya Kashe Budurwa sakamakon rashin amincewa da Soyayyar sa

Wani Matashi 'Dan Shekara 25 ya Kashe Budurwa sakamakon rashin amincewa da Soyayyar sa

A cikin wani sabon rahoto da muka samu da sanadin shafin jaridar Vanguard, wata 'Dalibar ajin karshe a makarantar sakandire mai shekaru 19 a duniya, Chinyere Ebere, ta gamu da ajalin ta a hannun wani matashi dan shekaru 25, Saliu Oladayo.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan lamari na ta'addanci ya afku ne a babban birni na Akure dake jihar Ondo, inda wannan matashi Saliu ya burma kaifi cikin kirjin 'Dalibar a sakamakon rashin amincewa da amsar soyayyar sa.

Binciken hukumar 'yan sanda ya tabbatar da cewa, wannan matashi ya aikata ta'addancin ne a sakamakon wata 'yar hatsaniya da ta shiga tsakanin su, inda Saliu ya bayyana cewa ai daman sabon ta ne ci masa mutunci da zagi na kare dangi.

Wani Matashi 'Dan Shekara 25 ya Kashe Budurwa sakamakon rashin amincewa da Soyayyar sa
Wani Matashi 'Dan Shekara 25 ya Kashe Budurwa sakamakon rashin amincewa da Soyayyar sa

Hukumar 'yan sanda ta bayyana cewa, ire-iren wannan cin mutunci da Marigaya Chinyere ta saba yiwa Saliu a baynar jama'a ya sanya ya fusata da yin wannan aika-aika da sai tsamo-tsamo cikin jini makwabta suka zuba mata idanu ta karasa ba tare da ikon kai dauki a gare ta ba.

KARANTA KUMA: Leah Sharibu: Akwai rudu cikin sasanci da 'Yan Ta'adda - Lai Muhammad

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar 'yan sanda tuni ta damke Saliu domin gudanar da bincike na diddigi kamar yadda kakakin ta ya bayyana, Femi Joseph.

A na ta bangaren yayin ganawa da manema labarai, Mahaifiyar Chinyere mai sunan Lovely ta bayyana cewa, tana zaune kwatsam a cikin shagon ta na kasuwa yayin da wannan mummunan labari ya riske ta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel