Ana nan dai jiya Iyau: Gungun yan bindiga sun far ma kauyukan Birgin Gwari guda 4
Gungun yan bindiga sun kai farmaki a wasu kauyuka guda hudu dake makwabtaka da juna a karamar hukumar Birnin Gwari na jihar Kaduna, inda suka hallaka mutane da dama, inji rahoton jaridar Daily Nigerian.
Wannan harin dai ya faru ne a ranar Talata 25 ga watan Mayu da misalin karfe 5 na yamma, inda yan bindigan suka afka ma kauyukan Dakwaro, Sabon Gida, Mashigi da wani kauye dake gefen Dakwaro
KU KARANTA: Dakarun Sojin kasa sun yi ma mayakan Boko Haram diran mikiya, sun aika da 15 barzahu
Majiyar Legit.ng ta ruwaito dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa a majalisar wakilan Najeriya, Hassan Shekarau ne ya bayyana haka a zaman majalisar na ranar litinin, 14 ga watan Mayu.
Shekarau ya nemi gwamnati ta kai ma al’ummarsa agaji sakamakon yawaitan munanan hare hare da yan bindiga ke kaiwa a yankin Birnin gwari. Wani danbanga MalamUmar yace sun gano gawarwaki guda goma, sa’annan ya tabbatar da cewa yan bindigar sun kona gidaje da kayan hatsi da dama.
“Al’ummar kauyukan na bukatar kayan abinci, kayan sawa da wajen zama, amma fa duk da hare haren nan, mun yaba da kokarin gwamnatin tarayya da jami;an tsaro, musamman ta yadda suka jibge jami’an tsaro da dama don magance matsalar.” Inji shi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng