An kama Daraktan INEC da Sakataren sa da almundahanar kudi

An kama Daraktan INEC da Sakataren sa da almundahanar kudi

A ranar Larabar nan ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC, ta gurfanar da tsofaffin manyan jami'an hukumar zabe ta kasa reshen jihar Enugu. Amadi Simon da Nathan Owhor Oviri a gaban mai shari'a A. M Liman na babban kotun Enugu da laifuka 16 ciki harda wanda suka hada kai suka tafka almundahanar kudade

An kama Sakataren zabe da cin hanci
An kama Sakataren zabe da cin hanci

A ranar Larabar nan ne hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC, ta gurfanar da tsofaffin manyan jami'an hukumar zabe ta kasa reshen jihar Enugu. Amadi Simon da Nathan Owhor Oviri a gaban mai shari'a A. M Liman na babban kotun Enugu da laifuka 16 ciki harda wanda suka hada kai suka tafka almundahanar kudade.

DUBA WANNAN: Adadin mutanen Najeriya zai karu da miliyan 189 daga 2018 zuwa 2050 - UN

Ana zargin ma'aikatan biyu da kwashe Naira Miliyan 131,380,000 wanda hakan ya sabawa sashe na 18 na dokar hana cin hanci da rashawa ta shekarar 2011, da kuma sashe na 16 na shekarar 2012.

An gurfanar dasu ne sakamakon zargin da ake musu na raba kudin kamfen ga wasu daga cikin jami'an hukumar na jihar Enugu wanda suka karba daga Diezani Allison Madueke, tsohuwar ministan man fetur, don su juya sakamakon zabe.

"Bincike daga hukumar yaki da cin hanci da rashawa tace kudin da aka tura musu wani sashe ne na miliyan 450 da aka turawa jihar Enugu don gabatar da kamfen din PDP. "

Wadanda ake zargin sun musanta hakan. An bada belinsu akan Naira miliyan 5 da kuma shaidu akan kowanne guda daya daga cikin su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: