Kwastam sun kama Motoci masu tsada 30 da Tirelolin shinkafa a cikin sati 4 kacal

Kwastam sun kama Motoci masu tsada 30 da Tirelolin shinkafa a cikin sati 4 kacal

- Hukumar hana fasa kwauri ta kasa na cigaba da samun nasara a yakin da take da masu shigo da kaya ta barauniyar hanya

- A baya-bayan nan sun samu wata gagarumar nasarar cafke kayan Miliyoyin Naira

Sashin yaƙi da masu shigo da kaya ta ɓarauniyar hanya na jami'an Kwastam sun yi nasarar cafke wasu kayayyaki da aka shigo da su ta ɓarauniyar hanya a jiya.

Kwastam sun kama Motoci masu tsada 30 da Tirelolin shinkafa a cikin sati 4 kacal
Kwastam sun kama Motoci masu tsada 30 da Tirelolin shinkafa a cikin sati 4 kacal

Shugaban jami'an Kwastam ɗin shiyyar Legas Garba Uba Mohammed ne ya bayyanawa manema labarai hakan jiya a Abuja, sannan ya ce sun samu nasarar karɓo ƙarin wasu kuɗaɗen da Mutane suka ƙi biyan hukumar bayan sun shigo da kaya har Naira Miliyan N28.9.

KU KARANTA: EFCC ta damke wani Sanata da ya karbi motocin naira miliyan 303 daga hannun barayin gwamnati

Muhammad ya cigaba da lissafa kayan da jami'an suka kama waɗanda suka kunshi: Toyota Prado Jeep da Range Rover da Toyota Hilux guda bakwai da Ford Edge, sanan kuma sun kama buhun shin kafa 5,516 kimanin Tireloli 9,sun a katan 1,078 na Taliya da kama Kaji da dangoginsu har guda 216 da kuma Jarkar man girki 683, sun ƙara kama Tayoyin Mota waɗanda anyi amfani da su tare da kuma tabar wiwi buhu takwas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng