Majalisar Dinkin Duniya zata dauki mataki akan kisan Falasdin da Isra'ila tayi
Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta gudanar da taron gaggawa bayan bukatar da Kasar Kuwait na ayi duba ga irin kisan kiyashin da ake yiwa al'ummar musulmi a zirin Gaza, inda a kwanan nan kasar Isra'ila ta kashe mutane 62 ciki kuwa hadda kananan yara babu gaira babu dalili
Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta gudanar da taron gaggawa bayan bukatar da Kasar Kuwait na ayi duba ga irin kisan kiyashin da ake yiwa al'ummar musulmi a zirin Gaza, inda a kwanan nan kasar Isra'ila ta kashe mutane 62 ciki kuwa hadda kananan yara babu gaira babu dalili. Wakilan kasashen duniya a majalisar dinkin duniya sunyi jimamin mutane da aka kashe a wajen zanga-zangar.
A jawabin da wakiliyar kasar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Nikey Haley tayi tace, suna cikin damuwa matuka akan halin da yankin na Gabas ta tsakiya ke ciki da kuma kisan mutanen da kasar Isra'ila tayi a yayin zanga-zangar da Falasdinawan suka yi a zirin Gaza.
DUBA WANNAN: Labari mai dadi: Gwamnatin Tarayya ta bada aikin hanyar Kano zuwa Bauchi
Tace, ana samun rikici sosai a yankin inda ta zargi Kwamitin da nuna halin ko in kula da kuma munafurci. Haley ta dora alhakin kashe-kashen akan kasar Iran.
Ta zargi kasar Iran da tayar da zaune tsaye a kasashen Labanan, Siriya, Yaman sannan kuma akwai bukatar a mayar da hankali akan kasar ta Iran indan har za ayi batun rikicin Gabas ta tsakiya.
Wakilin kasar Ingila Karen Pierce kuma cewa yayi kasar Isra'ila tana da hakkin kare iyakokinta amma kuma akwai bukatar sojin kasar su daina amfani da karfi da ya wuce misali.
Wakilin kasar Rasha a Majalisar Dimitry Polyansky ya bukaci Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da Abbas dasu sasanta junan su tare da kawo karshen matsalar da ake fuskanta yankin.
Wakilin Faransa François Delattre yayi gargadi akan yiwuwar rikicin ya yadu zuwa sauran yankunan.
Wakilin China Ma Zhaoxu, yayi kira ga kasar ta Isra'ila data nutsu ta kuma daina kashe Falasdinawa.
Wani jami'i na musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan samar da zaman lafiya a gabas ta tsakiya Nikolay Mladenov ya soki amfani da karfin soji da kasar ta Isra'ila tayi akan Falasdinawa.
A karshe wakilin Falasdin Riyad Mansur, yayi fashin baki inda yace, shin Falasdinawa nawa ne ake jira kasar Isra'ila ta kashe kafin Kwamitin Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya ta dauki wani mataki mai kyau, yanzu da ace a kasashen kune aka kashe mutane sama da 60, wadanda suka hada da yara kanana shin me zaku yi akai? Wannan bakin munafurcin har zuwa yaushe zai kare?
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng