Abincin da ya kamata mai azumi ya rika ci a Watan Ramadan
Yayin da aka shiga Watan Ramadan a Najeriya da kasashen Musulmai na Duniya mun tattara mun kawo maku dabarun cin abinci a cikin wannan Wata na Azumi. Gidan Jaridar Al-Jazira ta fara kawo wadannan dabaru.
A halin yanzu kusan dai an shiga Watan Ramadan a fadin Duniya inda Musulmai kusan Biliyan 2 za su yi azumi. Wasu dai su kan tagayyara yayin da su ke azumin don haka mu kawo wadannan dabarun cin abinci da za su taimaka.
1. Yawaita shan ruwa bayan buda-baki
Masana sun bada shawarar a rika yawaita kwankwadar ruwa sosai musamman cikin dare bayan an yi buda-baki. An so a sha akalla Lira 2 na ruwa bayan rana ta fada musamman a wuraren da akwai zafi. Da sahur ma an so a sha ruwa sosai.
KU KARANTA: Abubuwa 5 da ake tunani su na karya azumi amma ba su karyawa
2. A guji amfani da abinci mai gishiri da sahur
An kuma so wanda yake azumi ya nemi abincin da zai ba shi karfi da katabus lokacin sahur. A irin haka an fi son irin abubuwan da ba za su yi saurin narkewa a jikin mutum ba kafin a je ko ina. Sai a nemi irin su kunun oat da burodin alkama dsr.
3. A rika amfani da dabino da shan-ruwa
Da zarar an sha ruwa zai yi kyau mutum ya nemi dabino da ruwa da kuma abinci nigari. Ana son a ci irin su dankali ko shinkafa tare da ganye da nama ko kifi.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng