Musulman Kasar Holland za su yi sa’a 20 da azumi a bakin su

Musulman Kasar Holland za su yi sa’a 20 da azumi a bakin su

Kusan dai an shiga Watan Ramadan a fadin Duniya inda Musulmai kusan Biliyan 2 za su yi azumi. Mun kawo maku wasu Kasashen da za su dauki dogon lokaci kafin su karya azumin su saboda yanayin lokacin faduwar rana da fitowar Alfijir.

Ga dai jerin Kasashen da za su dauki kusan awa 20 da azumi a bakin su:

1. Kasar Iceland

Musulman Kasar Iceland za su yi awa 22 da azumi a bakin su a wannan shekarar don kuwa ana yin buda baki ne wajen 12:00 na dare sannan kuma Alfijir ya keto kafin karfe 2:00 na daren.

2. Kasar Norway

Haka kuma Mutanen Kasar Norway za su yi sama da awa 20 da azumi a rana. Ana shan ruwa a Kasar ne da karfe 10:30 na dare kuma Alfijiri ya keto da karfe 2:00 cikin dare.

KU KARANTA: Guzurin Ramadan: Abubuwa 5 da ke karya azumin Musulmi

3. Kasar Rasha

A Rasha ma dai sai Musulmai sun yi kusan awa 20 da azumi a bakin su. A Rasha ana ganin Alfijiri ne bayan karfe 1:30 na dare kuma ba za a sha ruwa ba sai bayan karfe 9:00 na dare.

4. Kasar Netherlands

Mutanen Netherlands za su yi awa akalla 19 da azumi a bana. A kan gama sahur ne tun kafin karfe 3:00 na dare kuma ba za a sha ruwa ba sai karfe 10:00 na dare. Kasar Denmark tana wannan sahun.

5. Kasar Ingila

Mutanen Kasar Ingila za su dauki kusan awa 19 su na azumi. Tun kafin karfe 3:00 na dare ake gama sahur amma ba za a sha ruwa ba sai bayan karfe 9:00.

Irin su Faransa, Jamus, Sifen da Italiya dai su kan yi awa akalla 17 da azumi. Najeriya da kasashe irin su Kasar Afrika ta Kudu ba za su wuce sa’a 14 su na azumi ba a rana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng