Shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen Manzo a wannan watan

Shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen Manzo a wannan watan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga daukacin Musulmai dama dukkanin 'yan Najeriya baki daya dasu yi iya bakin kokarin su don ganin sun taimaka wurin kawo karshen matsalolin da suka yiwa kasar nan katutu

Shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen Manzo a wannan watan
Shugaba Buhari yayi kira ga musulmai da suyi koyi da halayen Manzo a wannan watan

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga daukacin Musulmai dama dukkanin 'yan Najeriya baki daya dasu yi iya bakin kokarin su don ganin sun taimaka wurin kawo karshen matsalolin da suka yiwa kasar nan katutu. Shugaban kasar yayi kiran ne a ranar Larabar nan, a wani kira da yayi al'ummar kasar nan akan azumin watan ramadana na wannan shekarar.

DUBA WANNAN: Jinjina ga Almajiri ajin Farko: Alhaji Isiyaka Rabi'u

Babban mai taimakawa shugaban kasa akan fannin sadarwa Malam Garba Shehu, shine ya sanar da hakan, a wata sanarwa, inda yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci dukkanin musulmai dama 'yan Najeriya baki daya dasu dinga tunawa da talakawa marasa karfi a wannan watan.

Shugaban kasar ya mika sakon gaisuwar shi da kuma murna ga dukkanin ilahirin al'ummar musulmai na Najeriya dama na duniya baki daya da shigowar sabon watan azumi na wannan shekarar.

"Azumi ba wai ana yin shi kawai domin a kame daga yin wasu abubuwa na rayuwa ba, a'a wata dama ce da Allah ya bawa bayin sa domin gyara halayen su, da kuma kusan ta kansu dashi," inji shugaban kasar.

Ya kuma bukaci dukkanin al'ummar musulmi dasu kara dakkon soyayya a junan su, su dinga bayar da sadaka, kyautatawa juna, da dai sauran ayyukan alkhairi.

Ya ce ya fahimci cewar shugaban halitta Annabi Muhammadu (S.A.W) yana tausayawa talakawa a dai-dai irin wannan lokacin wurin ciyar da wadanda basu da shi. Shugaban kasar yayi kira ga dukkanin musulmi dasu yi koyi da halaye irin na Manzo.

A karshe shugaban kasar yayi addu'ar Allah ya bawa dukkanin musulmi ikon gabatar da ibadar su a tsunake a wannan wata mai albarka.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel