Shugaba Buhari ya saki kudi domin yashe kogin Kwara don arewa ta karbi jiragen ruwa

Shugaba Buhari ya saki kudi domin yashe kogin Kwara don arewa ta karbi jiragen ruwa

- A baya Ummaru Yaraduwa ya ware kudi don yin hakan

- An dakile shirin bayan rasuwarsa a 2010

- Arewa zata mora muddin aka jawo ruwan teku arewa

Shugaba Buhari ya saki kudi domin yashe kogin Kwara don arewa ta karbi jiragen ruwa
Shugaba Buhari ya saki kudi domin yashe kogin Kwara don arewa ta karbi jiragen ruwa

Zaman majalisar kasa na wannan mako, ya sahale sakin biliyoyin nairori, wadanda za'a yi amfani dasu don jawo teku zuwa arewacin kasar nan har zuwa jigar Neja, dama sayo wasu jiragen ruwa da kudin Turai Yuro 21m don jawo jiragen maqare da kaya zuwa arewa.

Ministan Sufuri shine ya bada wadannan bayanai a yau laraba, bayan zaman na majalisar kasar, inda ya fayyace yadda za'a fara aikin, wanda a baya shugaba Ummaru Yar'aduwa ya saki kudi don ayi, amma daga rasuwarsa, wanda ya gaje shi, ya dakile aikin.

A ci gaba da ake sa rai zai aru, don saukaka cunkoso a gabar tekun ta kudu, da saukaka wa arewa shigo da kaya har yankin cikin sauki, inda za'a fara sauke kaya a Baro ta jihar Neja.

DUBA WANNAN: Ta'aziyyar Sheikh Isiyaka Rabiu

Za dai a fadada wasu yankuna na ruwan na Neja, wanda aka baiwa wani kamfani Biara Concept Nig. Ltd.

A gefe guda kuma, za'a samar da gada a garin Karu, sai aikin ruwa a jihar Bauci da Calabar, da wasu manyan tituna da zasu hado kudu da arewar kasar nan. Yawanci ayyukan shekaru biyu zasu dauka ana yi.

Saura dai shekara daya wannan tarago na mulki ya kare, shuwagabannin su mika mulki ga wasu zababbu, ko kuma su zarce a karo na biyu in an zabo su.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng