Tsawon Rayuwata Ukuba ce daga Ubangiji - Inji wata Tsohuwa mai shekaru 128 a Duniya
Mun samu rahoto da sanadin shafin jaridar The Punch cewa, wata tsohuwa tukuf 'yar kasar Rasha ta bayyana cewa arziki na tsawon rayuwa da Mai Duka ya bata uƙuba ce kurum a gare ta ba wani abu ba.
Koku Istambulova, tsohuwar wadda ta shekara 128 a duniya da ta fito daga yankin Chechnya ta bayyana cewa, ba ta taba samun kwanciyar hankali ko jin dadi a rayuwar ta ba wanda a yanzu take mamakin yadda ta rayu cikin wannan yanayi kawowa yanzu.
Tsohuwar wadda ta shafe tsawon rayuwarta tana tone-tone cikin lambu ta bayyana cewa ta gajiya, hakazalika wannan tsawon rayuwa da ta samu ba wani abu bane face ukuba ta Ubangiji.
A yayin tunano yadda ta taso cikin rayuwa, tsohuwar ta bayyana cewa ta so ace tun tana da kananun shekaru ta koma ga Mahaliccin ta sakamakon gajiya ta aikace-aikace da shafe rayuwar ta tana aiwatar wa.
Legit.ng ta fahimci cewa, Koku ta shafe rayuwar ta tana aikin lambu da tone-tone domin shukar kankana, inda take korafin ba ta samu wata dama ta yin nishadi ko walwala a rayuwar ta ba.
KARANTA KUMA: Hameed Ali ya yiwa ma'aikatan Kastam gargadi akan neman Kudi a madadin jajircewa bisa aiki
Hukumomi na kasar Rasha sun bayyana cewa, takardun shaidar haihuwa na wannan dattijuwa tuni aka rasa su yayin yakin Chechen na biyu da ya afku a tsakanin shekarar 1999 zuwa 2009.
Cibiyar fansho ta kasar ta bayyana cewa, akwai ire-iren wannan dattijuwa kimanin 37 da shekarun su suka haura 110, sai dai tabbatar da hakan ya samu nakasu sakamakon takardun su na haihuwa da suka dade da salwanta.
Koku dai ta bayyana cewa, a halin yanzu babu abinda ke mata dadi a rayuwa face sarrafaffiyar madara inda tuni tayi hannu riga da ta'ammali da nama yayin da take sa ran cikar ta shekaru 129 a duniya a watan gobe.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng